Babu Wani Alkali Da Ya Isa Hanani Magana  -Nmandi Kanu Shugaban kungiyar fafutukar tabbatar da kasar Biyafara ta IPOB, Nmandi Kanu yace babu wani alkali ba ya isa ya hana shi magana da yan jaridu.

A ranar 25 ga watan Afirilu Mai Shari’a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya dake Abuja ta bada belinsa bisa sharadin bazai gana da yan jaridu ba,  kuma bazai shiga taron jama’a da suka kai goma ba. 

Kanu wanda yabi umarnin kotun kwanaki kadan bayan ya samu yanci daga zaman gidan yarin da yayi na watanni 18.

Tuni ya saba dukkanin ka’idojin da aka gindaya masa na sharadin belin, amma mai fafutukar yace shugaban kasa Muhammad Buhari da kuma shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS,Lawal Daura sune yakamata akalla a matsayin wadanda basa bin umarnin kotu. 

Yafadi haka a Enugu lokacin da yake karbar kyautar girmamawa daga wasu kungiyoyin kabilar Igbo.

“Alkalin kwararriya ce sosai saboda haka baza ta hanani magana ba,” yace. 

Da aka tambayeshi ko maganar da yakeyi da yan jaridu  tamkar saba umarnin kotu ne na kada yayi magana da yan jaridu Kanu yace “Ina baka ansa ne, abinda nake yi kenan yanzu,bawai Ina magana ne da yan jaridu ba a’a ko kadan ina dai baka ansa ne akan tambayar da kayimin.

  “Buhari da shugaban hukumar DSS sune suka  saba umarnin kotu da yawa. Ina fata zakaje ka DSS ka tambayi ko ma waye sunansa,Darakta Janar na hukumar kaji meyasa baya bin umarnin Kotu.”

You may also like