Bada Fifiko Kan Harkar Noma Da Gwamnatin Buhari Ta Yi Ya Taimaka Wajen Saukaka Kalubalen Abinci
A wata hira ta musamman da VAO a gefen taron, Shamsuna ta bayyana cewa bayan marawa Buhari baya, sun kuma je taron ne domin su nemi abokan hulda da zasu zuba hannun jari a Najeriya, su bude sabbin kamfanoni ko karfafa masana’antu don habbaka tattalin arzikin kasar.

Galibi shugabannin da suka halarci taron sun yi magana a game da kuncin tattalin arziki da ke shafar kasashensu, musamman hauhawar farashin abinci.

Shamsuna ta ce duk da cewa matsalar ta shafi Najeriya, tashin farashin abinci a kasar da sauki ba kamar wasu kasashe ba. Dalili kuwa shi ne, shekaru bakwai da shugaba Muhammadu Buhari ya yi yana mulki, an bada fifiko wajen bunkasa harkar noma, abin da ya sa ba sai an shigo da abinci ba domin a ciyar da ‘yan kasar, a cewarta.

“Duk da haka akwai damuwa game da tsadar abinci a Najeriya, saboda hauhawar kudin man fetur da dizel ya sa dakon kayan abinci daga gonaki zuwa kasuwanni ya kara tsada, amma sayen abincin a hannun manoma da dan sauki,” in ji Shamsuna.

A game da ciwo bashi da Najeriya ke yi, Shamsuna ta ce gwamnati ta karbo basussukan ne don tamaka wa ‘yan kasa, misali kamar a lokacin annobar COVID-19, lokacin da aka bukaci kudi don asibitoci, samar da kayan aikin kariya daga cutar, da killace mutanen da suka kamu da cutar, da kuma taimaka wa marasa karfi don su samu saukin matsin da annobar ta kawo.

Saurari hirar da Sarfilu Hashim Gumel ya yi da Ministar:

You may also like