Badakalar cin hanci a hukumar tsaro ta intanet – DW – 11/20/2023Kiev ta sanar da korar jami’in mai suna Iouri Chtchygol wanda ya share shekaru uku yana shugabancin hukumar sadarwar ta musamman da ke da alhakin ba da kariya ga ma’aikatun gwamnati kan abin da ya shafi internet da shi da mataimakinsa kan zargin yin sama da fadi da kudaden da yawansu ya kai miliyan daya da dubu 500 na kudin Euro.   

Karin bayani: Ukraine ta yunkura don yaki da cin hanci 

Ofishin mai gabatar da kara na Ukraine da hukumar bincike ta kasar sun ce, jam’in ya yi zamba cikin aminci da wadannan makudan kudi ne a tsakanin shekarar 2021 zuwa 2022, lokacin da zai cefano wata manhaja daga wata kasar waje. To sai dai daga nasa bangare jami’in ya musanta wannan zargi da ake yi masa, tare da cewa a shirye yake da ya kare kansa a gaban shari’a.

Karin bayani:  Daura danbar yaki da cin hanci a Ukraine

Kasar Ukraine ta yi kaurin suna a fannin cin-hanci da rashawa, koda a baya-bayan an bankado badakala makamanciyar wannan a tsakanin hukumomin soja lamarin da ya yi awon gaba da ministan tsaron kasar na waccan lokaci.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like