Badakalar Naira Miliyan 700: Kudin Na Siya Wa Sarkin Musulmi Gida Ne A Abuja – Gwamnatin Jihar Sokoto


Hukumar EFCC ta na binciken shugaban Ma’aikata na fadar Sarkin Musulmi Abubakar, sarkin Fadan Sokoto Kabiru Tafida kan wata boyayyiyar harkalla ta musanyar kudi naira miliyan 700 daga asusun gwamnatin jihar Sokoto zuwa asusun sa.
An saki Kabiru Tafida bayan matsi da hukumar EFCC ta samu daga gwamnatin jihar Sokoto da fadar Sarkin Musulmi.

Tun ranar Talatar da ya gabata ne hukumar ta gaiyaci Tafida da ya baiyana a hukumar domin bata bayanai kan harkallar shiga da ficen wadannan kudade.

Wani majiyar mu ya ce kudin an debesu ne daga kudin nan na Paris Club da aka rabawa jihohi.

“ Dalilin da ya sa muke tuhumar Tafida shine ganin bai taba yin aikin gwamnati ba sannan gashi sai tura manya manyan kudade akeyi asusun sa. Sannan an gano yana amsar kudade masu yawa wa Sultan.”

Gwamnatin jihar Sokoto ta ce wannan kudi za ayi amfani da sune don siya wa sarkin Musulmi gida a Sokoto.

“Sarkin Musulmi bashi da gida a Abuja, dalilin haka ne ya sa gwamnatin Jihar ta samar da wadannan kudade domin siya masa gida a babbar birnin tarayya .” Inji Gwamnatin Jihar Sokoto

You may also like