Bafarawa Ya Nuna Fushinsa Ga EFCC Kan Badaƙalar Milyan 600


Tsohon Gwamnan Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya nuna fushinsa ga hukumar EFCC kan yadda ta maka shi kotu kan badakalar milyan 600 na kudaden makamai a yayin da kuma hukumar ta ki tuhumar sauran wadanda suka karbi adadin wadannan kudade.

Bafarawa ya fayyace cewa an ba shugabannin PDP shida na shiyya shiyya wadannan kudade amma kuma ba a tuhume su sai shi inda ya bayyana cewa akwai Cif Jim Nwobodo daga shiyyar Kudu maso Gabas wanda shi ma ya karbi milyan 600, sai tsohon Shugaban PDP, Ahmadu Ali, Peter Odili, George Bode.

You may also like