
Asalin hoton, Getty Images
An yanke wa ‘ya’yan wata ƙungiyar bunƙasa addini da al’adun gargajiya ta Bahrain, hukuncin ɗauri a gidan yari.
Ƙungiyar dai tana rajin a riƙa tattaunawa a bayyane kan batutuwan addinin Musulunci.
An gurfanar da su ne a gaban kotu ƙarƙashin wata doka da ta haramta “aibata” duk wani littafin addini da Bahrain ke martabawa, waɗanda suka ƙunshi Ƙur’ani da Linjila.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam sun ce an musguna wa mutanen ne saboda sun bayyana ‘yancinsu na faɗar albarkacin baki da abin da suka yi imani da shi.
Ƙungiyar ta ce al’amarin ya harzuƙa wasu mutane har sun auka wa ‘ya’yanta da tashe-tashen hankula.
A cikin jerin shirye-shiryen da take wallafawa a shafin sada zumunta na YouTube, ƙungiyar Al-Tajdeed ta yi tambayoyi a kan matanan shari’ar Musulunci da ra’ayoyin malaman addinin Musulunci.
Ƙungiyar dai ta mabiya ɗariƙar Shi’a, wadda mafi yawan al’ummar Bahrain ke bi ce, duk da yake masu mulkin ƙasar mabiya Sunni ne.
Sai dai manyan malaman Shi’a ne suka fi fitowa fili suna nuna adawa da ƙungiyar, inda suke watsi da ayyukanta a matsayin saɓo har ma sun riƙa kira da ware ‘yan ƙungiyar ta Al-Tajdeed daga cikin al’umma.
Masu shigar da ƙarar, wadda daga ƙarshe aka kai kotu don ƙalubalantar ƙungiyar, sun ce an gurfanar da mutanen a kotu ne “saboda bijire wa hanyar addini madaidaiciya” kuma a “hana tawaye a cikin al’umma”.
Sun nemi a yanke wa waɗanda aka yi ƙara hukunci mafi tsanani a ƙarƙashin dokar Bahrain.
Al-Tajdeed – wadda ke nufin sabuntawa a harshen Larabci – ta maida martani a kotu da cewa: “Tunani, ana ƙalubalantar sa ne da tunani, don haka bai kamata a yi amfani da ƙarfin ikon doka a murƙushe kalaman fatar baki ba”.
A yanzu kotun ta yanke wa mutanen uku da aka yi ƙara – Jalal al-Qassab, Redha Rajab da kuma Mohammed Rajab – hukuncin zaman gidan yari na shekara ɗaya da kuma cin tara.
An jingine hukuncin har zuwa lokacin da za a saurari ɗaukaka ƙara.
Asalin hoton, Getty Images
Masallata na karatun Ƙur’ani a Bahrain
Al-Tajdeed ta ce shari’ar ta ta’azzara wani gangami da ake yi a masallatai da kafofin sada zumunta, da ke ƙarfafa gwiwar a auka wa ‘ya’yan ƙungiyar a magance da kuma a aikace.
A lokacin gudanar da shari’ar, ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Human Rights Watch ta yi kira, a yi watsi da tuhume-tuhumen kuma a dakatar da kalaman harzuƙa jama’a don su riƙa Allah-wadai da ƙungiyar Al-Tajdeed saboda dalilai na addini.
Bahrain tun tale-tale ta shahara a yankin Gulf, da kasancewa ƙasa mai karɓar mabambantan addinai da ɗariƙu da suka sha bamban. Ta buɗe coci mafi girma a yankin mai suna, Our Lady of Arabia Cathedral, a 2021.
Tana da al’ummar Yahudawa waɗanda kawai suka yi saura a yankin Gulf.
Sai dai, an daɗe ana sukar tarihinta na kare haƙƙin ɗan’adam saboda wariyar da take nunawa ga ‘yan Shi’a masu rinjaye a ƙasar.
Hukumomi sun musanta haka, sai dai har yanzu ana ci gaba da hana babbar ƙungiyar adawa ta ‘yan Shi’a mai suna Al Wefaq shiga zaɓuka.