Baje kolin motocin dake amfani da wutar lantarki a Paris


jpg_2216-1

 

 

Kanfanonin dake kera motoci sun gabatar da sanfarin motocin dake amfani da wutar lantarki a yayin bikin baje kolin da ake yi a birnin Paris, ciki har da motar da zata ci kilomita 400 ba tare da an yi mata chaji ba.

Katafaren kamfanin Volkswagen ya jagoranci gabatar da motocin wajen bikin baje kolin na Paris, inda yake sa ran dawo da tagomashin sa sakamakon matsalar da ya samu bara na boye yadda motocin sa ke fitar da hayaki.

Motar da kamfanin ya gabatar mai amfani da wutar lantarki na iya cin zagon kilomita 600 ba tare da an yi chanjin ta wato daga shekarar 2020.

Shugaban kamfanin Mathiaas Mueller yayi alkawarin gabatar da sama da kala 30 na motocin dake amfani da wutar lantarki nan da shekara ta 2025.

Shima kamfanin Opel da na Chevrolet Bolt duk sun gabatar da motocin su masu cin kilomita 400.

Kamfanin Renault na Faransa shima ya gabatar da sabuwar motar sa mai cin kilomita 400 wanda ci gaba ne daga wanda ake amfani da shi yanzu dake cin kilomita 240.

You may also like