Bakin Haure 35 Ake Fargabar Sun Rasa Rayukansu A Gabar Ruwan Kasar Libiya 


Hoto:Reuters

Bakin haure 35 ake fargabar sun rasa rayukansu bayan da jirgin da suke ciki ya nutse a gabar ruwan kasar Libiya a cewar jami’an tsaron gabar ruwa. 

Bakin haure 85 da suka hada da mata  18 an samu nasarar ceto su da taimakon masu kamun kifi, wadanda suka sanar da jami’an tsaron gabar ruwa, a cewar Issa al-zarrouk wani jami’in tsaron gabar ruwa a Garabulli,dake Kilomita 60 a gabashin Turabulus. 

 Mai magana da yawun sojin ruwan kasar, Ayoub Kacem yace jiragen kamun kifi goma ne suka taimaka wajen ceto mutanen.

 Bakin hauren da aka ceto sun fito ne daga kasashen Najeriya, Ghana, Kamaru, Kodebuwa da kuma kasar Senegal, kasim yace. 

Wata mai gyaran gashi da ta fito daga Najeriya mai suna Vivian Effousa ta bayyana kaduwarta ganin yadda yan uwanta fasinjoji suke nutsewa cikin teku.

  “Jirgin da muka shiga yana zubar da ruwa, ” a cewar Effousa dake kokarin isa nahiyar Turai a kokarin da take na tallafawa yayanta biyu dake gida Najeriya. 

 “Ba muyi tsammani ba kawai sai muka ga ruwa na shiga cikin jirgin, kawai sai kowa yafara Ihu.

” A hankali muka samu kan mu cikin teku, kowa na fadawa  ciki,  da na san haka teku take da girma da bazan baro kasata ba,” Effousa tace. 

A duk shekara dubban bakin haure ne daga kasashen Afirika kudu da hamadar Sahara ke yinkurin isa nahiyar  Turai.  

You may also like