Bakin Haure Kimani 400 Suka Tsallaka Kan Iyakar Kasar Morocco Da Espania Ta Ruwa


4bkc8f5000f431j19y_800c450

 

Bakin haure yan kasar Morocco kimani 400 suka tsallaka mashigar ruwa tsakanin Morocco da espania suka shiga tarayyar Turai.

Tashar television ta Presstv ta nakalto jami’an tsaron kan ruwa na kasar Espanai suna fadar haka a yau jumma’a sun kuma kara da cewa duk tare da shingen waya mai kayoyin karfe da aka kakkafa kan iyakokin kasashen biyu amma bakin hauren suna haurawa su shiga tarayyar ta Turai daga kan iyakoki na birnin Ceuta da kuma birnin Tapestry na kan iyakokin kasashen biyu.

Labarin ya kara da cewa mutane da dama daga cikin bakin hauren sun kasa hawa kan wayoyin sun kuma samu raunuka masu tsanani wadanda ya kasu jinya a asbitoci a biranen.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da dama suna sukan jami’an tsaron ruwa na kasar ta Espania da mummunan mu’amalar da bakin hauren.

Dubban darruwan mutane daga kasashen Afrika da Asia ne, wadanda suke fama da tashe tashen hankula ko kuma matsatsi suke tsallakawa zuwa tarayyar turai duk tare da cewa da dama daga cikinsu suna mutuwa a kan hanyarsu ta yin hakan.

You may also like