Bakin Kishi Ya Sa Dalibi Ya Yanka Makogwaron Masoyiyarsa A Jihar Adamawa. Wani dalibi a sashin Walwala da yawon bude ido da ke makarantar  Adamawa State Polytechnic , Yola (SPY), ya yanka makogwaron masiyiyarsa saboda tsabar bakin kishi. Dalibar wacce ake kira da Ishaya na karatu bangare guda da masoyin nata da aka fi sani da Presido, yayi mata aika-aika ne bayan ganin ta a motar wani da ya yi zargin ya kwace masa ita. 


Ya yi mata kwanton bauna a kusa da dakin dalibai mata tare da lakada mata dukan tsiya, kana ya dauko wuka ya farde mata makoshi. Duk da dai ta rayu amma tana mawauyacin hali a asibitin kwararru na Yola.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like