Bakuwar Cuta Ta Kashe Mutane 21 a Jamhuriyar Niger


 

agadez-cattle-market05

 

Jami’an kula da lafiya a Jamhuriyar Niger sun sanar da bullowar wata bakuwar cuta a yankin Tahoa da ke kasar. Izuwa yanzu, jami’an sun ce an cutar ta hallaka mutane 21.

Sun kuma bayyana cewa ana daukar cutar ne daga jikin dabbobi musammam idan aka sha nonon dabbar da ke dauke da ita.

Cutar wacce ba’a san irin ta ba ta billa ne a kasar a ‘yan kwanakin nan da suka gabata kuma tana ta yaduwa.

Hukumomin Niger sun ce suna yin iya kokarinsu wajen shawo kan cutar da ganin cewa an dakile yaduwar ta cikin gaggawa.

 

You may also like