Bam Ya Hallaka Mutane Da Dama A Jihar Adamawa A safiyar yau  Jumma’ ne Bama-Bamai uku suka fashe a garin Madagali na jihar Adamawa inda hakan ya yi sandiyyar rasa rayukan mutane da dama.
Majiyarmu ta tabbatar da cewa ababen fashewan sun fashe ne a cikin wats tasha dake cike da mutane a garin na Madagali.
Kawo yanzu babu tabbacin adadin mutanen da suka rasa rayukansu. 
Garin na Madagali dai ya kasance garin da ‘yan Boko Haram suka fi yi wa illa a jihar Adamawa. 
Wannan ba shine karo na farƙo da aka samu fashewan bam ba tun bayan sake bude garin da rundunar sojojin Nijeriya suka yi.

You may also like