Bam Ya Tashi A Garin Borno inda yai Sanadiyyar Rasa Ran Mutum 9


Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta tabbatar da mutuwar wasu mutane tara sakamakon tashin bam din da ya auku a yau Talata.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, Mista Victor Isuku ya bayyana cewa wadanda suka rasun suna cikin mota guda ne (a kori kura) a lokacin da bam din ya tashi.
Isuku ya kuma kara da cewa bam din ya tashi ne da misalin karfe goma da rabi naa safe a daidai shingen tsaro na sojoji dake kan titin Gubio.
Ya kara da cewa karin bayani kan aukuwar lamarin zai biyo bayan an kammala gufanar da bincike.

You may also like