Bam Ya Tashi Da Soja Daya Da Wasu Mutane Biyu a Jahar NigerWani mummunan tsautsayi da ya faru a jahar Niger ya haddasa rasuwar wani sojan Nijeriya tare da ‘yan uwansa guda biyu.


Shi dai wannan soja ya je jahar Niger ne ganin gida daga Maiduguri inda yake daya daga cikin wadanda ke yaki da mayakan Boko Haram.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jahar Niger Bala Elkalla ya bayyana cewa al’amarin ya faru ne yayin da sojan yake baiwa ‘yan uwan nasa labarin yadda suke yaki da Boko Haram a dajin Sambisa, kuma a lokacin da ya ke hakan akwai karamin Bom a hannunsa wanda ya ke nuna masu.

Toh da ya ke abun ya zo da ajali, sai wannan bom ya tashi, ya kuma kashe gaba daya su ukun.

Elkalla ya ce, tsautsayi ne kawai ba harin ta’addanci ba.

You may also like