BamBancin Aisha Buhari Da Patience Johnathan. 


  • Jonathan ya zama shugaban kasa mafi shan sukar siyasa, amma Patience kullum burinta mijinta ya ƙara ci gaba da mulkin Nijeriya.

  • Buhari ya zama shugaban ƙasa mafi farin jinin siyasa, amma Aisha ta ce ba za ta ƙara cewa a zaɓe shi ba.
  • Patience ta yi amfani da kafafen yaɗa labarai wajen cin zarafin ƴan Arewa don kiran su Almajirai kuma sakarkarun da ke haifar ƴaƴa suna jefarwa a titi.

  • Aisha ta yi amfani da kafafen yaɗa labarai domin ƙasƙantar da mijinta a matsayin lusarin da ya riƙe ƙahon Saniya wasu na tatsar nonon.
  • Patience ta kare mijinta a yayin da ake yi mana kisan kiyashi, muka rasa aminci muka samu abinci.
  • Aisha ta kwarewa mijinta baya a lokacin da muka rasa abinci muka samu aminci.

  • Patience ta goyi bayan mijinta a yayin da ya dakatar da shirin Marigayi ƴar adu’a na tono teku zuwa Arewa.
  • Aisha ta muzanta mijinta a matsayin wanda baya aikin komai a lokacin da ya samo mai a Arewa. Ya samo ma’adinan Nickel a Kaduna.
  • Patience ta zama matar shugaban ƙasa mafi rashawa a Nijeriya amma ba ta nadama.
  • Aisha ta zama matar shugaban ƙasa da mijinta ke son hana ta zama ƴar rashawa amma nadama ta ke yi.
  • Patience ta goyi bayan Jonathan domin ɗauko riƙaƙƙun ƴan ta’adda irin su Tampolo, Asari Dakubo, Edwin Clark suka riƙa kamfatar dukiyar ƙasa suna yi mana barazanar duk wanda bai zaɓi mijinta ba sai sun hana mu zama lafiya.
  • Aisha na adawa da Mamman Daura da Abba Kyari don sun hana dumbular dukiyar ƙasa.

You may also like