Majalisar koli kan tattalin arzikin Najeriya ta ce ba ta goyi bayan kiraye-kirayen da wasu suka yi ba na a sayar da wasu kadarorin kasar domin maganace matsalar komadar tattalin arzikin da kasar ta samu.
A ranar Laraba ne dai shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Bukola Saraki ya yi kira da a sayar da kadarorin kasar.
Kadarorin da ake magana a kai sun hada Kamfanin Sarrafa Iskar Gas na NLNG da Kamafanin Mai na kasar NNPC da dai sauran su.
To sai dai a zaman da Majalisar koli kan tattalin arzikin Najeriya ta yi na ranar Alhamis, ta ce ba ta goyi bayan kiran ba.
Amma kuma Majalisar ta ce ta goyi bayan shirin gwamnatin tarayya na farfado da karayar tattalin arzikin da kasar ta samu.
Majalisar, wadda ta kunshi gwamnonin jihohin kasar ta kuma yi watsi da kiraye-kirayen da wasu ‘yan majalisar dattawan kasar suka yi, na a cire ministocin kudi da na kasafi.
‘Yan majalisar dattawan Najeriya dai sun yi kira da sauya ministocin bisa zargin gazawa wajen farfado da tattalin arzikin kasar.