Kungiyar Kwadago a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, ta ce ba ta amince da soke sunayen ma’aikata dubu tara da gwamnatin ta yi.
Gwamnatin dai na zargin cewa ma’aikatan dubu tara na bogi ne wadanda aka dade ana karbar albashi da sunansu.
Da farko dai ma’aikata 13,000 ne ake zargin na bogi ne, kafin kuma daga bisani a tantance dubu hudu.
Sai dai kuma Kungiyar Kwadago a jihar ta ce ba za ta sabu ba wai bindiga a ruwa.
Kungiyar dai ta ce ba abu ne mai yiwuwa ba ace dukkannin ma’aikatan dubu tara na boge ne.
Karin bayani
Ma’aikatan boge dai wata hanya ce da wasu ke yin amfani da sunan wasu ma’aikata domin baba-kere da kudaden gwamnati.
Kusan za a iya cewa matsala ce da dukkan matakan gwamnati suke fuskanta, walau dai kananan hukumomi ko jiha ko kuma a tarayya.
Gwamnatin tarayya ta ce tana samun rarar kudi Naira Biliyan takwas a kowane wata sakamakon soke sunan ma’ikatan boge guda 400,000.