Gwamnatin Najeriya ta musanta baiwa mayakan kungiyar Boko Haram wasu kudade domin a sako mata ‘yan matan makarantar Chibok 21 da aka sako cikin watan jiya.
Cikin wata sanarwa kakakin shugaba Mohammadu Buhari, Alhaji Garba Shehu ya ce kafofin yada labarai dake baza wannan labari babu gaskiya a ciki.
Wannan maida martani na zuwa ne bayan da Rundunar Sojan kasar ita ma ta musanta cewa babu biyan kudaden fansa kafin a saki ‘yan matan Chibok 21 da aka kubutar da su.
Wata kafar yada labarai dake Nigeria ta fara sanar da cewa sai da Gwamnatin Muhammadu Buhari ta biya kudade da suka kai Dollan Amurka miliyan 21 kafin a saki ‘yan matan, kuma wai da kudaden ne kungiyar Boko Haram ta sayi makamai da take ta barna dan tsakanin nan.