Bamu Da Cikakken Rahoto Kan Harin Da Aka Kai Marantar Ƴan Mata A Yobe – Lai Mohammed


Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya bayyana cewa har yanzu gwamnati ba ta samu cikakken rahoto kan makomar daliban makarantar ‘yan Matan garin Dapchi a jihar Yobe bayan wani farmaki da mayakan Boko haram suka kai a Makaranta.

Tun da farko, an samu rudani bayan da gwamnatin Yobe ta ce an ceto dalibai 48 amma kuma daga baya ta musanta wannan rahoto, lamarin da ya harzuka iyayen yaran. Har yanzu dai, ba a san makomar dalibai 111 na makarantar wadanda ake tunanin mayakan Boko Haram din sun arce da su.

Sai dai kuma kamfanin dillanci Labaru na Ingila ya ruwaito cewa dalibai biyu sun rasa rayukansu a yayin da sojoji ke kokarin ceto su daga ‘yan Boko Haram a ranar Litinin da suka kai farmakin.

You may also like