Bamu da masaniyar cewa wani makiyayi ya kashe kansa – Rundunar yan sandan Benue


Yan sanda a jihar Benue sun ce rundunar bata da masaniyar cewa wani Bafulatani ya hallaka kansa bayan da ya rasa shanu kusan 200.

Wata jarida ce ta jiyo shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah dake jihar Garus Gololo na cewa wani Bafulatani dake ƙaramar Hukumar Logo ya kashe kansa ta hanyar fadawa ruwa bayan da ya rasa shanu masu yawan gaske.

A ganawar da yayi da jaridar Gololo ya dora alhakin mutuwar mutumin kan dokar hana kiwon dabbobi a fili da aka fara amfani da ita a jihar da ta jawo mutuwar dabbobin nasa saboda yunwa.

Amma kuma mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Moses Joel Yamu, ya ce rundunar bata da masaniyar faruwa ko rashin faruwar lamarin.

Yamu ya ce rundunar baza ta iya tabbatar da labarin ba ko kuma ta musalta faruwar shi saboda ba akai rahoton faruwar lamarin ba gaban baturen yan sanda na ƙaramar Hukumar Logo.

 

You may also like