Mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ya kara jaddada cewa gwamnatin tarayya bata da niyyar kara farashin kuɗin mai a shekarar 2018.
Mista Osinbajo ya bada wannan tabbaci ne lokacin da yakai ziyara wuraren da ake ajiye mai dake Lagos.inda ya duba yadda ake raban man zuwa gidajen mai daban-daban.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya rawaito cewa Osinbajo ya ziyarci manyan wuraren da ake ajiye mai da kuma wurin masu ruwa da tsaki a harkar samar da mai dake Apapa da kuma sauran wurare dake jihar Lagos a ranar kirsimeti.
A cewar mataimakin shugaban kasar matsalar karancin mai dake addabar ƙasarnan ta samo asaline daga karancin samar da man zuwa wuraren da ake ajiye shi.
Ya kuma ce duk wani dillali da aka samu yana boye man domin samun karin riba zai fuskanci hukunci daga hukumomin da abin ya shafa.