A Bamu Dama Mu Kamo Abubakar Shekau – Mafarauta


images-11

 

 

Kungiyar mafarautan Nijeriya ta bayyana cewa mambobinta za su iya mamaye dajin Sambisa su cafko shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau da ransa idan za’a basu dama.

Garba Tarfa wanda ke kula da harkokin tsaro na kungiyar a jahar Adamawa ya bayyana cewa mafarautan da dama a shirye suke, jira kawai suke a basu dama.

Garba wanda dan sanda ne mai ritaya ya kara da cewa sun san lungu da sako na dajin, kai sun san inda Shekau din ma ya ke boye a cikin dajin.

Ya kara da cewa ‘yan kungiyar Boko Haram na tsoron su fiye da yadda suke tsoron rundunar sojojin Nijeriya saboda sun san sun san sirrin su.

Ya kuma bayyana cewa Shekau yana boye a wani guri wanda ake gadi da manyan makamai a cikin dajin kuma ana Kiran gurin da Parisa.

Garba ya ce a cikin watannin 3 da suka gabata, mambobinsu da ke aiki da sojoji sun karfafa hare hare a cikin dajin na Sambisa inda suka ceto mata da yara wadanda adadinsu ya kai 500 suka kuma hallaka ‘yan Boko Haram guda 50.

Ya ce da ace gwamnati za ta yi aiki da mafarautan toh da tabbas wannan rikici zai zo karshe.

You may also like