Shugaban Ya bayyana hakan a jawabin da yayi na Murnar Zagayowar Ranar haihuwar sa, inda ya kara da cewa wannan yanayin da kasar take ciki na matsalar tattalin arziki abu ne wanda su kansu basusan dashiba a yayin yakin neman zaben da sukai.
Ya kara dacewa, wannan abune daga Allah bawai gwamnatin su ce ta jawo hakan ba. Sannan ya roqi yan Najeriya da suci gaba da yiwa kasa addu’a domin al’amura su dawo dai dai.
Sannan yana yiwa ‘yan Najeriya Albishir din cewa, Akwai shirye-shirye da Shugaban kasar wato Muhammadu Buhari yakeyi naganin an chanza al’ amura kamar yadda sukai wa mutanen Najeriya alkawari. Wannan shine matsalar tattalin arziki na karshe da zai faru a Najeriya inji shigaba Muhammadu Buhari.
A ‘yan kwanakin nan ne dai farashin danyen man fetur yayi rugu-rugu a kasuwar duniya wanda kuma shine babbar hanyar samun kudin shiga a Najeriya.