Ban Goyi Bayan Karya Darajar Naira Da Karin Farashin Fetur Ba –  BuhariShugaba Muhammad Buhari ya kara jaddada kin amincewa da karya darajar Naira da kuma kara farashin kudin man fetur yana mai cewa a kan irin wannan matsayi ne aka hambarar da shi a kan mulkin shekarar 1985.
Shugaban ya kara da cewa a lokacin yana Shugaban mulkin soja kungiyar Bada lamuni ta IMF ta nemi ya karya darajar Naira amma ya ki amincewa da shawarar kungiyar wanda a kan haka ne aka kifar da gwamnati na tare da Garkame ne har na tsawon sama da shekaru uku.

yana mai cewa a matsayinsa na Shugaban farar hula, ba zai amince da daukar wannan mataki ba ko da kuwa zai kai ga hambarar da shi daga mulki.

You may also like