Ban Ki-moon Ya Damu Kan Karamcin Tallafi A Haiti


 

Babban sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon, ya nuna matukar damuwarsa dangane da karamcin tallafin ga al’ummar Haiti da bala’in guguwar nan da aka yiwa lakabi da Matthew ta shafa.

Mista Ban Ki-Moon, ya ziyarci kasar Haiti ne domin ya ja hankalin duniya akan irin barnar da mummunar guguwar ta haddasa inda sama da mutane 500 suka rasa rayukansu.

Saidai a cewar Mista Ban bai ji dadin yadda kasashen duniya basu samar da tallafin azo -a -gani ba ga al’ummar ta Haiti, tare da kira ga masu hannu da shuni dasu taimaka.

Babban abun damuwa dai shi ne yadda cutar amai da gudawa ko kwalera ke kara yaduwa a kasar ta Haitin saboda rashin tsaftataccen ruwan sha.

Tunda farko dai Mista Ban ya ce akwai bukatar agajin gaggawa mai yawan gaske daga kasashen duniya, bisa la’akari da yadda garuruwa da kauyuka suka shafe, yayinda mutane miliyan daya da rabi ke bukatar taimakon gaggawa daga sauran al’umma.

You may also like