Ban ki-moon ya koka kan halin yaran Yemen


Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya sanya Saudiyya a sahun kasashe da ke buris da mawuyacin hali da kananan yara ke ciki sakamakon yaki a kasar Yemen.

 

 

Majalisar Dinkin Duniya ta koka kan yadda kawancen mayakan kasar Saudiyya ke fatali da matakan kare yara kanana a Yemen. Babban Sakataren MDD Ban-Ki Moon ya ce MDD ta sanya Saudiyya cikin jerin kasashen ke keta haddin yara kanana.
Wannan dai ya biyo bayan wasu rahotanni da kungiyyin kare hakkin ‘yan Adam suka wallafa, inda suka ruwaito cewar kawancen na Saudiyya sun halaka yara da dama yayin da sama da yara 1,200 suka gamu da munanan raunuka.
A watan Juni ne dai MDD ta sauke sunan kawancen yakin Amirka cikin jerin kasashen da ke cin zarafin yara, biyo bayan barazanar daina tallafa wa MDD da wasu kasashen da ke mara wa Amirkan baya suka yi.
Ban-ki Moon ya gana da manyan jami’an kasar Saudiyya don ganin sun dau kwararan matakai na jan kunne ga dakarunsu da ke yaki a Yemen dan kare hakkin kananan yara.

You may also like