Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo yace ba shine yakamata yafadi ranar da za a rantsar da ministocin da majalisa ta tantance ba.
Osinbajo ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da masu dauko rahoto daga fadar Shugaban bayan ziyarar da yakaiwa Buhari a birnin London.
Da aka tambayeshi ko yaushe ne za a rantsar da sabbin ministocin, Osinbajo sai yakada baki yace bashi ne yakamata ya fadi lokacin ba.
Majalisar dattawa ta tantance ministocin biyu Stephen Ocheni daga jihar Kogi da kuma Suleiman Hassan daga jihar Gombe, watanni biyun da suka gabata sai dai har yanzu Osinbajo ya gaza rantsar dasu.
Stephen Ocheni zai maye gurbin marigayi James Ocholi tsohon karamin minsitan kwadago wanda yarasa ransa a hatsarin mota kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, yayin da Suleiman Hassan zai maye gurbin tsohuwar ministar Muhalli Amina Muhammad wacce ta samu mukamin mataimakiyar shugaban majalisar dinkin duniya.
Amma mukaddashin Shugaban kasar yace nan bada jimawa ba za a rantsar da ministocin.