Ban Satar Wa Najeriya Ko Sisi Ba – Diezani 



Tsohuwar Ministar Kudi, Misis Diezani Alison-Madueke ta fito fili ta wanke kanta daga zargin almundahanar kudaden mai inda ta nuna cewa hukumar EFCC na amfani da kafafen Yada Labarai wajen bata mata suna sakamakon kin yin raddi da ta ki yi a tsawon wannan lokaci.
Ta kuma musanta cire dala milyan 153 daga asusun kamfanin mai na kasa(NNPC) a lokacin tana Minista inda ta kuma fayyace cewa rukunin gidajen da EFCC ta yi ikirarin mallakinta a jihar Bayelsa, na danginta ne wanda aka gina tun a shekarar 2011. Ta nuna takaicin yadda aka rika yayata cewa ta mayarda gwamnati wadannan dala milyan 153 alhali ita ba ta da masaniya game da kudaden.

You may also like