Ban Taba Tunanin Tsayawa  Takarar Shugaban Kasa Ba- Osinbajo 


Mataimakin shugaban kasa,Yemi Osinbajo, wanda ya kasance mukaddashin shugaban kasa na tsawon lokaci a cikin wannan shekarar yace bai taba tunanin tsayawa takara ba a shekarar 2019.

Najeriya dai  na fuskantar rashin tabbas kan ko  shugaban kasa Muhammad Buhari na da shirin tsayawa takara a kakar zabe ta 2019, Buhari mai shekaru 74 wanda ya karbi mulki a shekarar 2015 amma kuma ya kasance cikin jinya na lokaci mai tsawo cikin wannan shekara. 

Osinbajo mai shekaru 60 kuma kwararren lauya ya kasance a matsayin mukaddashin shugaban kasa na  tsawon lokaci da Buhari ya kwashe yana jinya. 

  A tsawon lokacin da yayi a matsayin mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ya kawo sauye-sauye da dama da jama’a ke ganin hakan zai iya bashi damar tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2019.

Amma da jaridar Financial Times ta tambayeshi  a birnin London  a wurin taron kasashen Afirka da aka yi kan cewa ko yana duba yiyuwar tsayawa takara Osinbajo yace bai taba tunanin haka ba a takaice ma wannan baya cikin tsarinsa.  

Osinbajo ya kuma ce yanzu yan  bindigar yankin Niger Delta basa kawo barazana ga man da Najeriya take fitarwa. 

You may also like