BAN UMARCI FULANI SUKAI HARIN FANSA A NUMAN BA – SARKIN MUSULMI


Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Saad II ya jaddada cewa ba shi ya umarci Fulani su kai harin fansa a garin Numan da ke jihar Adamawa a jiya Litinin ba.

Tun bayan rikicin ne, Sarkin Musulmi ya fito fili ya yi gargadin cewa kada a dauki hakurin makiyaya a matsayin rauni, kalaman da ake ganin sun harzuka Fulani wajen kai hare haren Fansan.

A jiya ne aka fafata tsakanin makiyaya Fulani wadanda suka kai harin fansa a wasu kauyaku da ke kusa da garin Numan a jihar Adamawa yankin da  ‘yan kabilar Bachama suka yi wa Fulani kisan Kiyashi kwanaki.

You may also like