Ban yi katsalandan ko tsoma baki a zabukan da suka gabata ba — Shugaba BuhariMuhammadu Buhari

Asalin hoton, OTHER

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ya yi matuƙar gamsuwa da irin rawar da ya taka a zaɓukan ƙasar da suka gabata, ta hanyar ƙin yin wani katsalandan ko tsoma baki.

Shugaban mai barin gado ya ce ɗokin da ‘yan Najeriya suka nuna wajen zaɓa wa kansu mutanen da za su shugabance su ba tare da wani ya tsoma musu baki ba, manuniya cewa lallai dimokraɗiyyar Najeriya ta kawo ƙarfi.

Cikin wata tattauna da BBC ta yi da mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu, ya ce ya ji dadi matuka saboda ‘yan Najeriya sun zabi abin da rans uke so.

Ya ce su ‘yan Najeriya idan har an ba su dama su zabi abin da suke so ba tare da an ce ga abin da zasu zaba ba, to suna zaben abin da suke so ne.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like