Bani da niyyar canza magana kan batun ‘yan matan Chibok –  Buhari


Matsalolin da ke addabar Najeriya da ‘yan kasar ba wani sabon labari bane, shin me gwamnati ke yi domin magance wannan matsala da Najeriya ke ciki? Tambayar kenan da Sashen Hausa na Muryar Amurka ya yiwa shugaba Mohammadu Buhari.
A cewar shugaba Buhari, akwai matsalar tattalin arzikin kasa da rashin aikin yi ga matasa, kuma anyi sa a damuna tayi kyau bana, wanda babban bankin tarayya ya hada kai da ministan sha’anin aikin Gona Mr. Abdu Ogbeh su kayi iyakar kokarinsu, wanda yan Najeriya sun san irin nasarar da aka samu.

Sai kuma batun cin hanci da rashawa, inda shugaba Buhari yace wannan zamanin da muke ciki ya banbanta da zamanin shekara ta 1984, wanda a wancan lokacin aka tattara wadanda ake zaton sunyi zalunci aka kaisu Kiri-Kiri. Yanzu dole ne sai an gudanar da bincike an samu shaidar da za a gabatar gaban kotu kafin a hukunta su, kuma wannan shine ka kawo koma baya.

Game da batun ‘yan matan Chibok da kuma tsagerun Niger Delta, Buhari yace yayi magana har sau uku kuma bashi da niyyar sake yin magana kan batun ‘yan matan Chibok, har sai shugabannin Boko Haram sun fito kafin a shiga yin wata magana.

Ya danganta da tsagerun Niger Delta inji Buhari, in suna son a sasanta da su sai a sasanta idan kuma ba sa so sai a zuba.

You may also like