Shugaban kasar Banizuwela Nicolas Maduro ya ba da umarnin mamaye cibiyar kamfanin Kimberly -Clark na kasar Amirka dake aikin sarrafa takardu da sauran kayan tsabtace muhalli a kasar
Shugaba Maduro ya tilasta wa kamfanin na Kimberly-Clark gudanar da aiki bayan da kamfanin ya dauki mataki dakatar da aikinsa a ranar Asabar da ta gabata a sakamakon a bisa a cewarsa matsalar matsalar tattalin arziki da kasar ta Banizuwela take fuskanta.
Shugaba Maduro ya dauki wannan mataki ne a matsayin martani ga abinda ya kira yinkurin kasar Amirka na neman durkusar da tattalin arzikin kasar ta Banizuwela ta hanyar dakatar da ayyukan kamfanoninta da ke aiki a kasar ta Banizuwela.
Dama dai yau watanni biyu da suka gabata shugaban kasar ta Banizuwela wacce ke fuskantar matsalar tattalain arziki a sakamakon faduwar farashin man fetur wanda kasar ke tunkaho da shi, ya sha alwashin bude kofofin duk wani kamfani da zai dauki matakin dakatar da aiki a bisa hujjar matsalar tattalin arziki da kasar take fuskanta.