Nayi matukar bakin ciki da labarin harin bom a Maiduguri. Sakon ta’aziyya ta ga ‘yan uwan da abin ya shafa, da gwamnatin jihar Borno.
Rashin samun damar rike kowane garuruwa ya sa kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram wanda a yanzu suke kai harin kunar bakin wake na tsoro kan mutanen da basu ji ba, ba su gani ba.
Na yabawa rundunar tsaron mu kan irin namijin kokarin da suke yi. Wannan hari zai kara mana kaimi wajen kanin kawo karshen kungiyar ta Boko Haram gaba daya.
— Shugaba Muhammadu Buhari