Banki amsa kiran EFCC ba –  SHEMA


Tsohon gwamna Jihar Katsina ta arewacin Najeriya, Ibrahim Shehu Shema, ya yi musun cewa hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta neme shi ta rasa.
A jiya ne dai hukumar ta EFCC ta bayar da sanarwa cewa tana neman tsohon gwamnan ruwa a jallo don ya amsa tambayoyi game da wadansu makudan kudi da ake zargin ya yi sama da fadi da su.

A wata hira da ya yi da BBC, tsohon gwamnan ya ce a watan Disamban bara EFCC ta aiko mashi takardar gayyata, lauyoyinsa kuma suka bukaci sanin laifin da ya yi, amma hukumar ta ce ba ta yin haka.

“Suka sake rubutowa suka ba da lokaci, suka suna so in halarci wurinsu, a lokacin ba ni nan ina Ingila…. To da na dawo aka gaya mani, na ce to su ba mu rana za mu zo.

“Sai suka ba da rana…28 ga watan Yuni…. Ya kasance cikin watan azumi ne—na yi wa lauyana magana ya zo Abuja, ni ma na zo Abuja, muka dunguma za mu tafi ofishin EFCC karfe 10 na safe kamar yadda aka yi alkawari; sai muka samu bayani daga ofis din–wani ya buga mana waya cewa wadanda za mu je mu gani sun tafi Calabar, amma za a sake sa wata rana”.

Tsohon gwamna ya ce tun wancan lokacin, duk da lauyansa ya rubuta wa EFCC takarda yana neman a sa ranar ganawa da su 28 ga watan Agusta, ba su ji komai daga EFCC ba.

“Abin da kawai na samu labari shejaranjiya (Laraba) sun je gidana ba ni nan, suka dan kekkewaya, suka shiga suka dauki hotuna—karfe daya suka bar gidana, na samu labari; karfe biyar kuma aka buga a jarida da intanet cewa ana nema na ruwa a jallo”, inji Shema.

Tsohon gwamnan na Jihar Katsina ya kuma ce ba shi ba ne mutum na farko da aka kai gaban hukumar EFCC kuma ba shi ne na karshe ba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like