Bankin Duniya ya amince da ware dala miliyan 500, domin taimakawa Najeriya wajen inganta samar da hasken lantarki, shirin da ya kunshi bunkasa ayyukan kamfanonin dake aikin rarraba hasken wutar.
Cikin sanarwar da ya fitar Bankin Duniyar yace tallafin zai shafi kamfanoni masu zaman kansu ne kawai, dake rarraba hasken lantarki a Najeriya.
Wata kididdiga da bankin ya fitar ta nuna cewar akalla ‘yan Najeriya miliyan 85 ne ba sa samun hasken wutar lantarki, kwatankwacin kashi 43 cikin 100 na yawan al’ummar kasar.
Alkaluman na nufin a halin yanzu Najeriya ke kan gaba a duniya wajen fuskantar gibin rashin wadatar hasken lantarki, matsalar da masana suka ce tana haddasawa kasar hasarar kudaden shigar da yawansu ya kai dala biliyan 26 da miliyan 200, kwatankwacin naira Triliyan 10 duk shekara.