Bankin Raya Afrika zai taimakawa Najeriya da Dala biliyan 4.1


 

 

Bankin Raya Kasashen Afirka ya ce zai taimakawa Najeriya da kudin da ya kai sama da Dala biliyan 4, domin ta da komadar tattalin arzikin kasarta, wajen gudanar da manyan ayyuka da bunkasa noma.

Shugaban Bankin kuma tsohon ministan noman Najeriya Akinwumi Adeshina ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Adesina ya ce, Bankin zai gabatarwa Najeriya kudadde ta fannoni daban-daban da suka hada da samar da wutar lantarki, samar da kayan more rayuwa da kuma noma, da kuma tallafi ga kananan ‘yan kasuwa.

Shugaban Bankin wanda tsohon Ministan noma ne a kasar ya kuma bayyana fatar ganin alakar Bankin da Najeriya ta kara habaka maimakon raguwa, tare da fatar ganin an kara karfin tallafin da Bankin zai bai wa kasar nan da shekarar 2019 zuwa Dala biliyan 10.

You may also like