Bankin Unity Bank Plc Ya Kakkabe Ma’aikata Guda 215


reno

 

A jiya Laraba, bankin Unity Bank Plc ya kori ma’aikata akalla 215 a yunkurinsa na sauya dabaru da tsare tsaren aiki wanda zai karawa bankin daraja.

Rahotanni na nuna cewa an kori ma’aikatan ne a sakamakon gazawar da suka yi na jurewa da sabbin sauya sauyen da aka kawo game da yadda ayyukan bankin ke gudana.

Tun lokacin da bankin ya dauke babban ofishinsa daga Abuja zuwa Lagos ne ya shigo da wasu tsare tsare da suka kunshi janyo ma’aikata masu kwarewa a bangarori daban daban domin kara fadada yawan abokan cinikayyarsa.

Bankin a cikin shekara dayan nan ya dauki sabbin ma’aikata kusan 200 wadanda suka dace da sabon tsari na bankin, yayin da aka karawa kusan 100 girma.

Yanzu kuma bankin ya bukaci akalla ma’aikata 215 wadanda aka baiwa damar su yi murabus da kansu, da su bar aikinsu domin su baiwa kamfanin damar sauya akalar ayyukansa zuwa kan sabuwar hanyar da ya tanada.

You may also like