
Asalin hoton, AFP
Tsofaffin takardun kuɗin naira 1,000
Bankunan kasuwanci a Najeriya na ci gaba da korar masu kai ajiyar tsofaffin takardun kuɗin naira 1,000, da 500, da kuma 200.
Ga alama, matsalar ta yi ƙamari a sassan Nijeriya kamar Gusau, babban birnin jihar Zamfara, da ma wasu yankunan da dama.
A ranar Litinin BBC ta tattauna da wasu mazauna Gusau, inda mutanen suka ce sun rasa abin yi bayan da suka kai kuɗi banki aka ƙi karɓa.
Rashin karbar tsofaffin kuɗi ya jefa mutane cikin garari
‘Zan kwana da yunwa duk da ina maƙare da kuɗi’
Wani ɗalibi mai sana’ar ɗinki, Umar Musa ya ce dole ta sa zai kwana da yunwa, duk da dubban nairorin da ke maƙare da aljihunsa.
Yana kuma fargabar cewa a zai iya rasa damar rubuta jarrabawar gwaji a makaranta.
Ya ce “yanzu haka da nake magana ba ni da kuɗin mashin da zan hau na je makaranta. Ina da tsofaffin kudi a aljihuna amma ban san yadda zan yi na kashe su ba.”
Ya ƙara da cewa hatta masu sayar da abinci, kamar shayi da taliyar yara ba su fito ba “yanzu haka yunwa nake ji, na ce a daho min taliya amma ya ce ba zai karɓi sababbin kuɗi ba.
‘Har na cike takardar ajiye kuɗi aka ce ba a son tsofaffi’
Haka su ma wasu mazaunan na Gusau sun ce sun yi ta walagigi da dubban nairorinsu a tsakanin bankuna amma ba su iya samun ko banki ɗaya da ya karɓi ajiyarsu ba.
Wani mutum ya shaida wa BBC cewar har sai da ya cike takardar biyan kuɗi ta banki sannan aka shaida masa cewa ya haɗa ta da takardun aljihunsa ya koma.
Ya ce “mutane na ta yawo saman titi domin a amsa (tsofaffin takardun kuɗi) amma an ce ba za a amsa ba.”
Ya bayyana cewa ya zagaya bankuna huɗu amma babu inda aka karɓi tsofaffin kuɗin da ya je da su.
Ya ce a yanzu ana ƙarancin sababbin takardun kudi, bankuna kuma sun ce ba za su karɓi tsofaffi ba.
“Ina sayar da shinkafa, na tashi yau ina da kusan naira 100,000 amma na wuni ina ta tagayyara da su.”
Ya ce ya kuma je gidan mai domin ya sha a abin hawa amma an ce ba za a karɓi tsofaffin kuɗi ba.
‘Sun ce sai sun ji daga Babban Bankin Najeriya’
Mutanen da BBC ta zanta da su sun ce bayanin da bankunan ke yi musu shi ne sai sun ji daga Babban Bankin Nijeriya, kafin su ci gaba da karɓar tsoffin takardun kuɗin.
Ba dai jihar Zamfara ce kawai ke fama da irin wannan matsala ba domin rahotanni daga wasu jihohin na nuna cewa ana fuskantar irin wannan matsala a bankuna da kuma wasu masu sana’o’i
Matsalar na zuwa ne duk da umarnin wucin gadi na Kotun Ƙolin Nijeriya, wanda ya dakatar da Babban Banki da gwamnatin ƙasar daga aiwatar da niyyarsu ta daina amsar tsoffin takardun nairorin a matsayin halartattun kuɗi.
Da kuma tabbacin Shugaba Muhammadu Buhari na ganin al’amura sun inganta a cikin kwana 10.