Barayi dauke da makamai sun kashe mutane 27 a Birnin Gwari


Ba afi mako guda ba da kashe wasu masu hakar ma’adanai a kauyen Janruwa dake karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, mutane 27 aka sake kashewa ranar Asabar a kauyen Gwaska.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa yan bindiga da suka fito daga jihar Zamfara mai makotaka da jihar sune suka yi wa garin Gwaska kawanya har ya zuwa kauyen Kuiga da misalin karfe biyu da rabi na ranar Asabar inda suka shiga harbi ba kakkautawa tare da kashe mutane yawancinsu yara kanana.

Wakilin jaridar ya kuma gano cewa yan bindigar sun kuma kona garin baki dayansa da mutane sama da dubu uku ke rayuwa a ciki,wadanda kuma suka tsira da yawancinsu matane suna gudun hijira lardin Doka dake yankin.

‘Ya’yan karamar hukumar karkashin wata kungiya da ake kira Birnin Gwari Vanguards for Peace and Good Governace sun ce ” yawancin wadanda aka kashe yan sakai ne da suka yi kokarin kare kauyen da kuma kananan yara da baza su iya gudu ba.”

“Yan bijilante sun sanar damu cewa adadin wadanda suka mutu zai iya karuwa amma sun yi alkawarin tattaruwa a gobe domin debo gawarwakin wasu mutanen da lamarin ya rutsa da su.

Harin na ranar Asabar na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan da babban sifetan yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya kai ziyarar aiki karamar hukumar ta Birnin Gwari a kokarinsa na kawo karshen hare-hare dake faruwar a karamar hukumar.

You may also like