Rahotanni Daga Jihar Jigawa Na Nuni Da Cewa Barayin Mashina Sun Matsa Da Yawan Satar Mashinan Al’umma A Sassan Kananan hukumomin Jihar Jigawa,
Sai Dai Lamarin Yafi Kamari A Kananan Hukumomin Hadejia,Gumel,Mallammadori, Da Maigatari.
Ko a Watanin Baya Sai Da Barayin Mashin Suka Kashe Wani Dan Acaba A Garin Gumel, Kana Sukayi Awun Gaba Da Mashin Dinsa.
Lamarin Na Yawan Satar Mashin Ya Har Zuka Jami’an Tsaro A Jihar Jigawa, Inda Yanzu Haka Badare Ba Rana, Jami’an “Yan Sanda, Civic Defence Da “Yan Kato Da Gora Suna Ta Sintiri A Sassan Jihar Jigawa Domin Farautar Masu Satar Mashinan Al’umma.