Fadar Shugaban kasa ta zargi barayin gwamnati da shirya zanga zangar kin jinin Shugaba Buhari wanda wasu ‘yan Nijeriya mazauna birnin Landon suka gudanar a jiya Talata.
Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya ce tarzoman ba zai hana Shugaban cimma manufar ziyarar da ya kai Birtaniya ba inda ya nuna cewa mafi yawan masu zanga zangar, an yi hayarsu ne. Shugaba Buhari dai ya kai ziyara Birtaniya ne don tattauna batun dangantakar Kasahen biyu da Firayi Ministan Birtaniya, Theresa May.