Barayin Shanu Sun Mika Wuya A Katsina Sakamakon wani shirin afuwa da gwamnatin Katsina ta kaddamar  ga masu aikata miyagun laifuka, barayin shanu ne da dama suka fito suka mika wuya don cin gajiyar shirin afuwar.
Rahotanni daga jihar sun nuna cewa barayin Shanun sun mika makaman da ke hannunsu inda aka samu bindiga kirar AK47 har 104 sai kuma kananan bindigogi guda 267.

You may also like