Kimanin mutum 2000 ke gudun hijira a jihar Niger sakamakon ayyukan barayin shanu daga makwaftan jihohin Zamfara, Kebbi, Kaduna da Sokoto.
Da yake karin haske game da batun, Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na jihar Niger, Alhaji Ibrahim Inga ya ce gwamnatin jihar ta samar da matsuguni ga ‘yan gudun hijirar a kananan hukumomin Shiroro da Rafi tare da samar masu kayayyakin Jin kai.