Barazanar Fuskantar Hare-Haren Wuce Gona Da Iri A Yankin Gabashin DR Congo


 

 

Gwamnan lardin Kivu ta Arewa da ke gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ya yi gargadin cewa ‘yan tawayen kasar da suke da sansanoni a yankunan kasar Uganda kusa da kan iyaka da Dimokaradiyyar Congo suna shirin kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar lardinsa.

A taron manema labarai da ya gudanar a garin Goma fadar mulkin lardin Kivu ta Arewa; Gwamnan lardin Julien Paluku ya bayyana cewa: ‘Yan tawayen tsohuwar kungiyar M23 karkashin jagorancin Sultani Makenga da suka tsere cikin kasar Uganda suna shirye-shiryen kaddamar da wasu jerin hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Jamhuiriyar Dimokaradiyyar Congo da suke rayuwa a yankunan da suke kusa da kan iyaka da kasar ta Uganda.

Julien Paluku ya kara da cewa: Tun bayan fatattakan ‘yan tawayen kungiyar M23 daga cikin kasar Dimokaradiyyar Congo a cikin watan Nuwamban shekara ta 2013 suka kafa sansanoninsu a yankin Bunagana da ke cikin kasar Uganda kusa da kan iyaka da Jamhuriyar Dimokaradiyyar ta Congo.

You may also like