
Asalin hoton, Getty Images
Barcelona da Real Madrid za su buga wasa na biyu a daf da karshe a Copa del Rey ranar Laraba a Camp Nou.
Ranar 2 ga watan Maris Barca ta je ta ci Real 1-0 a Santiago Bernabeu a wasan farko, Eder Militao ne ya ci gida a minti na 26 da fara wasa.
Duk wadda ta yi nasara za ta fuskanci Osasuna a wasan karshe a Copa del Rey na bana ranar 6 ga watan Mayu.
Wannan shine karo na biyar da za a fafata a kakar nan tsakanin manyan kungiyoyin Sifaniya biyu, inda Real ta fara cin 3-1 a La Liga a Oktoban bara.
Barcelona ta dauki Sifanish Super Cup a kan Real Madrid da ci 3-1 a Saudi Arabia cikin watan Janairun 2023.
A watan Maris Barcelona ta doke Real Madrid 1-0 a wasan farko a Copa del Rel a Santiago Bernabeu.
Sai Barcelona ta ci Real Madrid 2-1 a La Liga a Nou Camp cikin watan Maris.
Wasa hudu da aka kara a El Clasico a bana
Sifanish La Liga Lahadi 19 ga watan Maris 2023
- Barcelona 2 – 1 Real Madrid
Sifanish Copa del Rey Alhamis 2 ga watan Maris 2023
- Real Madrid 0 – 1 Barcelona
Sifanish Super Cup Lahadi 15 ga watan Janairun 2023
- Real Madrid 1 – 3 Barcelona
Sifanish La Liga Lahadi 16 ga watan Oktoban 2022
- Real Madrid 3 – 1 Barcelona
Tuni Carlo Ancelotti ya bayyana ‘yan wasan da ya je da su Camp Nou domin buga wasa na biyu a Copa del Rey daf da karshe.
‘Yan wasan Real Madrid da suka je Camp Nou:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da Luis López.
Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V. da Rüdiger.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni da D. Ceballos.
Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo da Mariano.
Real za ta je Camp Nou da kwarin gwiwa, bayan da ta sharara 6-0 a ragar Real Valladolid a La Liga a karshen mako, inda Karim Benzema ya ci uku rigis.
Real za ta buga wasan tare da Rudiger, wanda ya sha jinya, dukkan ‘yan wasanta sun shirya fuskantar kalubalen El Clasico ranar Laraba, in banda Mendy.
Barcelona za ta karbi bakuncin Real, bayan da kungiyar Nou Camp ta je ta ci Elche 4-0 a karshen mako a La Liga.
Lewandowski ne kan gaba a yawan ci wa Barca kwallaye a bana mai 27 kawo yanzu har da 17 a La Liga.
Kawo yanzu Barcelona ta ci wasa 13 a Camp Nou da canjaras hudu aka doke ta karawa daya, kenan da jan aiki a gaban Real Madrid.
Barcelona ce ta daya a kan teburin La Liga da tazarar maki 12 tsakaninta da Real Madrid ta biyu.
Karim Benzema ya ci kwallo 14 a La Liga kawo yanzu.