Barca ta ce sai inda ƙarfinta ya ƙare a kan Messi, Chalsea na tattaunawa da LukakuLukaku

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool na son ɗauko ɗan ƙwallon tsakiya na Manchester City wato Kalvin Phillips da bazara kuma ɗan ƙwallon duniyar mai shekara 27 na ƙasar Ingila yana da damar tafiya. (Star)

Chelsea za ta tattauna da maharin ɗan ƙwallon Belgium Romelu Lukaku, wanda ya tafi zaman aro Inter Milan, inda za ta tambayi ɗan shekara 29 ko yana son komawa ƙungiyar tasu a ƙarƙashin sabon kocin da suke son ɗauka Mauricio Pochettino. (Telegraph)

Kocin wucin gadi na Chelsea Frank Lampard a shirye yake ya yi magana da Pochettino game da rukunin ‘yan wasan da ke bugawa ƙungiyar don taimakawa miƙa ragamar kulob ɗin da ake sa rai ga sabon koci ɗan ƙasar Argentinan ya tafi sumul ƙalau cikin nasara. (Evening Standard)

Tottenham, Chelsea da Manchester United na shirin daka wawa a kan ɗan wasan tsakiyar Portugal mai bugawa Fulham Joao Palhinha, mai shekara 27, a wannan bazara. (Football Insider)Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like