
Asalin hoton, Getty Images
Barcelona za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan mako na 26 a La Liga da za su kara a wasan hamayya na El Clasico ranar Lahadi a Nou Camp.
Wannan shine karo na hudu da za su fuskanci juna daga biyar da za su buga a tsakaninsu a wasannin Sifaniya.
Real Madrid ta fara cin 3-1 a gasar La Liga cikin Oktoban 2022 a La Liga a Santiago Bernabeu.,
Sai dai Barcelona ta lashe Sifanish Super Cup a Saudi Arabia a cikin watan Janairu da cin 3-1.
Haka kuma Barcelona ta ci Real Madrid 1-0 a wasan farko na daf da karshe a Copa del Rey da suka buga a Santiago Bernabeu a farkon makon watan Maris.
Ranar 5 ga watan Afirilu, Barcelona za ta kara karbar bakuncin Real Madrid a wasa na biyu na daf da karshe a Copa del Rey a Nou Camp.
Barcelona ce ta daya a kan teburin La Liga da maki 65, Real Madrid ce ta biyu mai 56, kenan da tazarar maki tara tsakani.
Robert Lewandowski na Barcelona kan gaba a cin kwallaye a La Liga mai 15, Karim Benzema na Real Madrid 11 ne da shi.
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Luis López.
Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V., Rüdiger da kuma F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni da kuma D. Ceballos.
Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo da kuma Mariano.
‘Yan wasan Barcelona 21 da za su fuskanci Real Madrid:
Ter Stegen, Araujo, Sergio, Gavi, Lewandowski, Ansu Fati, Ferran, Iñaki Peña, Christensen, Marcos Alonso da kuma Jordi Alba.
Sauran sun hada da Kessie, S. Roberto, F. De Jong, Raphinha, Kounde, Eric, Balde, Pablo Torre, Arnau Tenas da kuma Alarcón.
Wasa uku da suka buga a kakar bana:
Copa del Rey ranar Alhamis 2 ga watan Maris 2023
- Real Madrid 0 – 1 Barcelona
Spanish Super Cup ranar Lahadi 15 ga watan Janairun 2023
- Real Madrid 1 – 3 Barcelona
Gasar La Liga ranar Lahadi 16 ga watan Oktoban 2022
- Real Madrid 3 – 1 Barcelona