Barcelona da Granada sun raba maki a La Liga ranar LahadiBarcelona

Asalin hoton, Getty Images

Matashin ɗan wasa, Lamine Yamal ya ci wa Barcelona kwallo biyu a wasan da suka tashi 3-3 da Granada a gasar La Liga ranar Lahadi.

Mai shekara 16 shi ne ya fara ci wa masu masukin baki ƙwallo daga baya Ricard Sanchez ya farke daga kwallon da Facundo Pellistri ya bugo.

Daga baya ɗan kwallon Manchester United da ke wasa aro, Pellistri ya ci wa baki na biyu, sai dai Robert Lewandowksi ya farke.

Daga baya Ignasi Miquel ya ci wa Granada na uku, sai Yamal ya farkewa Barcelona.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like