Barcelona ta dauki mai tsaron baya Digne


Barcelona ta dauki mai tsaron baya, Lucas Digne daga Paris St-Germain kan kudi fan miliyan 13 da miliyan tara.

Dan kwallon wanda ya yi wa Roma wasanni 33 a matsayin aro, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar, da sharadin duk kungiyar da take son daukarsa, sai ta biya Barcelona fan miliyan 51.

Digne ya buga wa PSG wasanni 44, bayan da koma kungiyar da murza-leda a shekarar 2013 daga Lille.

Shi ne kuma dan kwallo na biyu da Barcelona ta sayo a bana, bayan da ta dauki Samuel Umtiti daga Lyon.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like